Isa ga babban shafi
Faransa

Jami'an kula da gidajen yari na yajin aiki a Faransa

An kulle ilahirin gidajen yarin da ke kasar Faransa, bayan wani yajin aiki da kungiyar ma'aikatan gidan yarin ta kira a yau litinin kan dalilan da ta bayyana da rashin biyan albashi, rashin tsaron ma'aikatan dama uwa uba walwala da jin dadinsu.Tuni dai ministan Shari'ar kasar ya kira wani taron gaggawa da shugabancin kungiyar don tattaunawa tare da lalubo hanyoyin magance matsalar. 

Wani babban gidan yari a birnin Paris na Faransa
Wani babban gidan yari a birnin Paris na Faransa PATRICK KOVARIK / AFP
Talla

Matakin yajin aikin na zuwa ne a dai dai lokacin da aka shiga mako na biyu da fara wata zanga-zangar lumana kan batun, inda ofishin da ke kula da ayyukan gidajen yarin karkashin ma'aikatar shari'a ya ce akalla gidajen yari 130 daga cikin 188 ne suka kasance a kulle yayinda ma'aikata da dama suka yi fito na fito da jami'an tsaron kasar.

Daraktan ofishin tafiyar da ayukan gidajen yarin ya bayyana cewa, a halin yanzu sun maida hankali ne wajen kara yawan jami'an tsaron, 'yan sanda da kuma Jandarmomi, a wasu gidajen yarin domin maye gurbin ma'aikatan da suka kauracewa aikin

A cewar kungiyar kwadagon ta UFAP-UNSA akwai kimanin jami'an gidajen yarin dubu 28 da suka shiga zanga-zangar bore da halin ko'in kula da ake nuna musu a kasar ta Faransa, ko da yake dai akwai da dama da aka yiwa barazana kan shiga zanga-zangar.

Sanarwar da ma'aikatar shari'ar ta fitar, ta ruwaito Nicole Belloubet ministan shari'ar Faransar na cewa akwai bukatar jami'an tsaron gidajen yarin su kasance masu kishin kasa kafin aiwatar da wani yunkuri da ka iya haddasa illah ga tsaron gidajen yarin.

Tuni dai Mr Nicole Belloubet ya bukaci tattaunawar gaggawa kai tsaye da manyan kungiyoyin kwadagon kasar 4 da suka kunshi ta UFAP-UNSA da CGT da kuma FO don lalubo bakin zaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.