Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar dattijan Amurka ta katse kudaden tafiyar da gwamnati

Majalisar dattawan Amurka ta gaza tattara kuri’u 60 da take bukata, don bata damar amincewa da kudurin ci gaba samar wa Gwamnatin tarayyar kasar kudadden gudanar da ayyukan ta.

Daraktan kasafin kudi na gwamnatin Amurka Mick Mulvaney yayin ganawa da manema labarai a wajen fadar White House a Washington. 19, Janairu, 2018.
Daraktan kasafin kudi na gwamnatin Amurka Mick Mulvaney yayin ganawa da manema labarai a wajen fadar White House a Washington. 19, Janairu, 2018. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Karo na farko kenan da irin haka ta faru a kasar, duk da cewa jam’iyyar Republican ke da rinjaye a majalisun kasar zalika shugaban kasar ma daga jam’iyyar ta Republican ya fito.

In banda sashin rundunar sojin kasar da kuma wasu ma’aikatu masu muhimmanci, gazawar tattaunawar na nufin yankewar kudaden tafiyar da gwamnatin tarayyar Amurka, da zai tilastawa ma’aikatu da hukumomin tarayyar, dakatar da ayyukansu da kuma biyan albashi.

Sakatariyar gwamnatin Donald Trump Sara Sanders ta zargi ‘yan jami’yyar Democrats da haifar da wannan rudani, sakamakon kafewar da suka yi wajen kare shirin kula da baki-hauren da ke kasar, da suka shiga a lokacin da suke kananan yara.

A ranar Alhamis din da ta gabata, ‘yan majalisar wakilan Amurka 230 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin ci gaba sa samar da kudaden tafiyar da gwamnatin kasar zuwa watan Fabarairu, yayin da ‘yan majalisar wakilan 197 suka kada kuri’ar kin amincewa da kudurin.

Sai dai kudurin ya gaza samun amincewar majalisar dattijan, inda ‘yan majalisar 50 suka hau kujerar naki, 49 kuma suka goyi bayan kudurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.