Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa: Gwamnati ta kawo karshen rikicin shekaru kan gina filin jirage

Gwamnatin Faransa, ta sanar da janye shirinta na gina sabon kafataren filin jiragen sama a birnin Nantes da ke yammacin kasar.

Sashin filayen da aikin gina sabon filin jiragen sama a birnin Nantes, da manoma a yankin Notre-Dame-des-Landes suka bai wa kariya, tare da hadin gwiwar kungiyoyin kare muhalli.
Sashin filayen da aikin gina sabon filin jiragen sama a birnin Nantes, da manoma a yankin Notre-Dame-des-Landes suka bai wa kariya, tare da hadin gwiwar kungiyoyin kare muhalli. AFP
Talla

Matakin ya kawo karshen kusan shekaru 10 da aka shafe, ana rikici tsakanin masu goyon bayan gina sabon filin jiragen, da wadanda ke adawa da shirin.

Yayin da yake sanar da janye shirin, Fira ministan Faransa Edouard Philippe ya ce zazzafar adawa da shirin sabon ginin ce ta tilastawa gwamnati janye aniyarta a birnin na Nantes.

Fira ministan ya ce a maimakon gina sabon filin jiragen, gwamnati zata fadada wadanda ake da su a yankin yammacin kasar ta Faransa, domin dai daita bukatar sufurin jiragen sama da ke dada karuwa a yankin.

Dubban manoman da aikin gina sabon filin jiragen zai shafa ne suka rika nuna zazzafar adawa kan aikin, inda suka hada kai da kungiyoyin kare muhalli bisa da’awar cewa aikin barazana ce ga muhallansu, hakan ta kai ga wasu daga ciki suka dauki makamai da nufin bai filayen da za’a aiwatar da aikin kansu kariya.

A zamanin gwamnatin Farancois Hollande aka gudanar da zaben raba gardama tsakanin al’ummar yammacin kasar ta Faransa dangane da ginin sabon filin jirgin a birnin Nantes, zaben da masu goyon bayan shirin suka yi rinjaye.

Sai dai wadanda ke adawa sun hau kujerar naki, inda suka rika gudanar da jerin zanga-zanga, wadda ta kai ga haddasa mummunar arrangama tsakaninsu da jami’an ‘yan sanda a shekarar 2012 inda sukai amfani da bama-baman gargajiya, da duwatsu wajen kai wa jami’an tsaron hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.