Isa ga babban shafi

Faransa ta karbi masu neman mafaka dubu dari a 2017

Sakamakon kididdigar hukumar kare ‘yan gudun hijira, ta nuna cewa Faransa ta karbi bakuncin masu neman mafaka dubu dari a shekarar da ta gabata.

Albaniyawa sun fi yawa daga cikin bakin da suka shiga Faransa, saboda yadda gwamnatin kasar ke daukar Albania a matsayin kasar da bata da masu haifar barazana ta fuskar tsaro.
Albaniyawa sun fi yawa daga cikin bakin da suka shiga Faransa, saboda yadda gwamnatin kasar ke daukar Albania a matsayin kasar da bata da masu haifar barazana ta fuskar tsaro. AFP/ by Claire GALLEN
Talla

Shekarar ta 2017, ta zama wadda aka fi samun kwarar baki cikin Faransa mafi yawa a tarihi.

Fitar da sakamakon binciken ya zo a dai dai lokacin da gwamnatin Faransa ke shirin gabatar da wata doka kan shigowar baki wadda ta haifar da zazzafar muhawara.

A wata mai kamawa ne gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron ke shirin gabatar da wata doka kan shigowar baki a kasar, sai dai akwai rarrabuwar kawuna tsakanin ‘ya’yan jam’iyyarsa game da dokar.

Shugaban hukumar da ke kare ‘yan gudun hijira Pascal Brice ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, Faransa na daga cikin kasashen da suka fi karbar masu neman mafaka a cikin nahiyar Turai.

Kididdigar ta nuna cewa Albaniyawa su ne suka fi yawa cikin bakin da suka shiga kasar, saboda Faransa na daukar kasarsu a matsayin wadda bata da masu barazana cikinta ta fuskar tsaro.

Sauran kasashen da ke da yawan masu neman mafaka a kasar ta Faransa sun hada da Haiti, Guyana da kuma Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.