Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa: Za a fara hukunta matan da ke auran mayakan Jihadi

Gwamnatin Faransa ta amince da matakin fara hukunta matan kasar da ke zuwa Syria domin auren mayakan Jihadi muddin za’a yi musu adalci.

Emilie König da ta fito daga wani yanki na kasar Faransa, wadda ta yi fice wajen daukar mayakan jihadi.
Emilie König da ta fito daga wani yanki na kasar Faransa, wadda ta yi fice wajen daukar mayakan jihadi. Reprodução Youtube
Talla

Matakin na Faransa ya zo ne yayin da muhawara ta barke kan makomar matan da ke tattaki zuwa Syria domin auren mayakan IS da ake ganin an karya lagonsu a kasar

A wannan makon labarin Emilie Konig mai shekaru 33 da ta fito daga wani yanki na Faransa kuma ta yi fice wajen daukan mayakan jihadi, ya ja hankali.

Konig dai ta kasance cikin matan nahiyar Turai na baya-bayanan da aka gano na wannan aiki kuma ake sa ran dawo ta gida.

Sai dai kakakin gwamnatin Faransa Benjamin Griveaux ya ce babu wani shirin da ake na dawo da ita kasar.

Jami’in ya ce indai akwai hukumomin shara’a da zasu tabbatar da adalci kan matan da ake cafkewa da basu daman kare kai to a yanke musu hukunci a can.

Benjamin ya ce duk girman laifin da Faransawa zasu aikata a ketare muddin akwai daman kare kai, basa shakan ayi musu shara’a amma sai an basu tabbaci.

Konig, wacce sunanta ke bayanen cikin jerin mutane da MDD da Amurka ta bayyana a matsatyin masu hatsari, an cafke ta ne cikin watan Disamba inda ake rike da ita a sansani kurdawa da yaranta kanana Uku da wasu Faransawa Mata da dama.

Lauyan Konig dai Bruno Vinay na ci gaba da ja-in-jan lallai Faransa ta dawo da ita gida karkashin dokokin kasa da kasa.

A shekara ta 2012 Matar wacce mahaifinta dan sanda ne ta musuluntata bayan auren mijinta na farko tare binsa Syria da barin ‘ya’yanta 2 a Faransa sai dai daga bisani an kasha shi.

Konig ta sha fitowa a fai-fan bidiyon Farfaganda da ake barazanar kai hari Faransa.

Akwai dai Faransawa 30 mata da maza da sojoji ke tsare dasu wanda ‘yan jihadi ne kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.