Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai kafa dokar yaki da labaran karya a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na shirin kafa wata doka da za ta yaki labaran boge ko karya a kafafan sada zumunta wanda ya ce na haifar da barazanar ga tsarin Dimokradiyar kasar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa REUTERS/Ludovic Marin/Pool
Talla

Shugaba Macron ya ce shi da tawagarsa sun fuskanci irin wannan barazanar ta yadda labaran boge da kutse a shafukansu lokacin gangamin yakin neman zabensa a bara.

Tun lokacin da ya kama mulki a watan Mayun shekara ta 2017, shugaban ke zargin kafar yadda labaran Rasha ta ‘RT Channel’ da yada labarai na boge a kansa ta shafukan Intanet da sada zumunta a lokacin Kamfe.

Macron da ke yi wa ‘yan jaridu jawaban sabuwar shekara ya ce, in dai ana son kare dimokradiya, tilas a kafa doka mai tsauri da kuma sauye-sauyen da zai kawo canji a rawar da kafafan yadda labaran Faransa ke takawa.

Dokar da macron ke son kafawa ta kunshi goge kalaman da aka wallafa na karya da kuma rumfe shafin mutumin da ya wallafa ko datse shi daga shiga yanar gizo.

Shugaban wanda alakarsa da kafafan yadda labarai ta sha ban-ban da ta tsohon shugaba Francois Hollande ya ce ya zama tilas jami’ai su nesanta kansu da ‘yan jaridu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.