Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kawo karshen bincike kan kisan tsohon shugaban Rwanda

Lauyoyin Faransa da ke yaki da ta’addanci, sun kawo karshan binciken da suke kan kisan tsohon shugaban kasar Rwanda Juvenal Habyarimana, da ake zargi an yi mafani da makami mai linzami wajen kakabo jirginsa.

Tun a shekarar 1994 ne aka yi mafani da wani makami mai linzami wajen kakabo jirgin shugaban kasar ta Rwanda Juvenal Habyarimana.
Tun a shekarar 1994 ne aka yi mafani da wani makami mai linzami wajen kakabo jirgin shugaban kasar ta Rwanda Juvenal Habyarimana. AFP
Talla

Wannan al’amari da ya haifar da kisan gilla a shekarar 1994 a Rwanda, ya kasance babban tashin hankali tsakanin kasashen Biyu sakamakon zargin da ake yi wa shugaban Rwanda Paul Kagame wanda shine jagoran mayakan Tutsi a wannan lokaci da harin ya faru.

Harin na Makami Mai linzami a kusa da filin jiragen saman Kigali ya haifar da mummunan rikicin kabilanci tsawon kwanaki 100 tsakanin kabilar Tutsi da Hutu, inda aka kiyasta mutuwar akalla mutane dubu 800.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.