Isa ga babban shafi
Brexit

Brexit: EU za ta bude sabon tattaunawa da Burtaniya

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da shiga mataki na gaba a tattaunawar da suke kan makomar alakarsu da Burtaniya da ke shirin ficewar daga cikinsu. Sai dai sun yi gargadin cewar ganawan wannan lokaci zai yi tsauri sama da na farko kafin su kai wannan matsayin.

Firaministan Burtaniya Theresa May da Shugaban Majalisar EU Jean-Claude Juncker
Firaministan Burtaniya Theresa May da Shugaban Majalisar EU Jean-Claude Juncker REUTERS/Yves Herman
Talla

Shugaban na EU, Donald Tusk ya ce kungiyar za ta bude tattaunawar tare da nazari mai zurfi da Burtaniya, sakamakon gamsuwa da yarjejeniyar wucin-gadi kan dokokin ficewar kasar daga cikinsu, wadda shine ya bude kofar sabon ganawa.

Tusk ya ce duk da yardarsu na shiga tattaunawar daga Janairu kan rabuwa da Burtaniya a tsawon shekaru 2, kulla yarjejeniyar kasuwanci ba zai soma ba sai a watan Maris.

Tusk da ke zantawa da Manema labarai a taron da suka karkare a Brussels yau Juma’a, ya ce yanzu lokaci ne na soma shirye-shiryen cikin gida a kungiyar da Burtaniya domin samun karin haske kan abin da suke fata. Amma ba lallai su cim-ma jituwar karshe kafin Maris din 2019 ba.

Shugaban ya taya Firaministan Burtaniya Theresa May murnar wannan ci gaba da aka samu.

Yarjejeniyar wucin-gadin da suka kula ya hada da na ‘yanci ‘yan kasa, iyakar Irish da daftarin dokar rabuwa da Burtaniya.

A sakon da ta aike a Twitter, May ta ce wannan ranar ce mai muhimmaci domin an samu ci gaba a kokarinsu na rabuwa da EU da makomarsu a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.