Zuwan firaministan Isra’ila a Faransa ya haifar da fushin faransawa dake goyan bayan batun zaman lafiya a yankin, sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ran su ga matakin da Shugaban Amurka ya dau na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.
Ana sa ran Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shawo kan Benjamin Netanyahu don gani ya yi watsi da bukatar shugaban Amurka.