EU ta shigar da karar mambobinta a kotu saboda baki
Kungiyar Tarayyar Turai ta shigar da karar kasashen Jamhuriyar Czech da Hungary da Poland a gaban babbar kotun nahiyar saboda yadda suka ki karbar wani kaso na ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin ya nuna jajircewar Kungiyar Tarayyar Turai wajen ganin cewa, mambobinta sun mutunta tsarin da aka samar a shekarar 2015 na karkasa ‘yan gudun hijira dubu 160 tsakanin kasashen Turai don rage nauyin da ke kan Girka da Italiya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Brussels, Hukumar Tarayyar Turai ta ce, ta yanke shawarar maka Jamhuriyar Czech da Poland da kuma Hungary a kotun shari’a saboda yadda suka yi watsi da hakkokin da suka rataya a wuyansu.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga bangaren wadannan kasashe da a can baya suka ce, tilasta mu su karbar wani kaso na ‘yan gudun hijirar, wani yunkurin tauye mu su ‘yanci tafiyar da kasashensu ne.
A cikin watan jiya ne , Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi daukan mataki kan kasashen bayan tsawon lokacin da aka shafe tana gargadin su.
Yanzu haka dai kasashen na fuskantar barazanar biyan tara mai yawa a kotun da ke Luxembourg.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu