Isa ga babban shafi
Faransa

Tsaffin shugabannin Faransa da Amurka sun gana kan yarjejeniyar yanayi

Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama da takwaransa na Faransa Francois Hollande sun yi wata ganawa a yau Asabar, inda suka tattauna kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris da kasashen duniya suka sanyawa hannu.

Barrack Obama ya yi fatar ganin Amurka ta koma cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris don gogayya da sauran kasashen duniya.
Barrack Obama ya yi fatar ganin Amurka ta koma cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris don gogayya da sauran kasashen duniya. REUTERS/Kamil Krzaczynski
Talla

Tsaffin shugabnnin biyu sun yi imanin cewa, Yarjejeniyar ta zama tamkar guguwar da babu wanda zai iya tsayar da ita.

Obama wanda ke ziyara a birnin Paris na Faransa sun tattauna ne tare da Francoise Hollande a wani Otel bayan kammala cin abinci.

shugabannin biyu, sun kuma bayyana fatarsu na ganin Amurka karkashin jagorancin shugaba mai ci Donald Trump  ta sauya matsayarta kan yarjejeniyar ta Paris don tafiya tare da sauran kasashe.

A baya-bayan nan ne dai shugaba Trump na Amurka ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar bayan tun farko kasar ta amince da batun karkashin jagorancin Barrack Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.