Isa ga babban shafi
Amurka

Micheal Flynn ya amsa laifin yi wa hukumar FBI karya

Tsohon mai bai wa shugaban Amurka Donald Trump shawara kan tsaro Micheal Flynn, ya amsa laifin yi wa hukumar binciken kasar FBI karya, na musanta zargin da ake masa na ganawa da Jakadan Rasha a Amurka, makwanni kafin Trump ya dare shugabancin kasar.

Tsohon mai bai wa shugaban Amurka Donald Trump shawara kan tsaro Micheal Flynn.
Tsohon mai bai wa shugaban Amurka Donald Trump shawara kan tsaro Micheal Flynn. REUTERS/Carlos Barria/File Photo
Talla

Mista Flynn shi ne mafi kololowar wanda ya rike mukami a gwamnatin Trump, da masu bincike ke tuhumar, yana da alaka da zargin ake yi wa tawagar yakin neman zaben Trump da hada kai da Rasha don tasiri a sakamakon zaben shugabancin Amurkan na 2016.

An fara tuhumar Flynn bayan fara aikin tawagar masu bincike da Robert Mueller ke jagoranta.

Manyan kafafen yada labaran Amurka sun rawaito cewa, cikin jawabin da Flynn ya yi wa masu binciken, ya ambata sunayen wasu manyan jami’an gwamnatin Trump, wadanda suke da hannu wajen hada kai da jami’an kasar Rasha don tasiri kan zaben da ya baiwa Trump nasara kan Hillary Clinton.

A halin da ake ciki kuma hankula sun koma kan surikin Trump kuma mai bashi shawara, wato Jared Kushner wanda ake kyautata zaton shi ne jami’i na gaba da za’a fara bincika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.