Isa ga babban shafi
Turai

Merkel na cikin tsaka-mai-wuya

Rikicin siyasar da Jamus ke neman fadawa zai hana gwamatin Merkel daukan matakai ko umarni a cikin gida da ma nahiyar turai baki daya har sai an sake wani sabon zabe.

Shugabar Jamus, Angela Merkel.
Shugabar Jamus, Angela Merkel. REUTERS/Axel Schmidt
Talla

Shugabar Gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta shiga tsaka-mai-wuya ne bayan rushewar kokarinta na kafa sabuwar gwamatin hadin-kai, lamarin da ke neman tursasa wa kasar sake gudanar da sabon zaben.

Merkel, wacce tsarinta na karban bakin haure ya gamu da tsananin rabuwar kawuna, dole ya sa ta ke neman kawance da wasu jam’iyyun, la’akari da cewa ba ta samu rinjiye a zaben kasar da ya gabata ba.

Sai dai bayan shafe sama da wata guda tana fadi-tashin ganin ta cim-ma yarjejeniyar, jam’iyyar FDP ta shure takalmanta a tattaunawarsu cikin daren jiya, tare da shaida cewa babu yarda a tsakaninsu.

Merkel dai ta jajirce cewa za ta yi duk mai yiwuwa domin fitar da kasar daga cikin wannan kangi.

Kazalika Shugaba Emmanuel Macron, da ke neman goyon bayan Merkel a kudirinsa na kawo sauye-sauye a EU, ya nuna damuwa da halin da siyasar kasar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.