Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta cimma yarjejeniya mai tsoka da Daular Larabawa

Shugaban Faransa Emanuel Macron ya sanar da cewa Faransa ta cimma yarjejeniya na kera wasu jiragen ruwan yaki 2 ga kasar Daular LarabawaKamfanin kera jiragen ruwan yakin na faransa ne, ya yi nasarar sabe kwangilar a gaban manyan abukan takararsa 2 na turai .

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Daular Larabawa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Daular Larabawa REUTERS/Satish Kuma
Talla

A ranar karshe ta ziyarar aikin da ya kai yankin Daular larabawa a jiya alhamis ne, shugaba Macron ya bayyana cewa, kasar ta yi nasarar samun wannan kwangila, inda kamfanin kera jiragen ruwan yakin kasar zai kerawa kasar ta daular larabawa dake yankin Gulf kasar da ta kasance abukiyar kawance ga Faransa .

Shugaban na faransa ya yi wannan sanarwa ne a lokacin wani taron manema labarai bayan ya gudanar da wata tattaunawa da yarima mai jiran gado Abou Dhabi, haka kuma mataimakin babban kwamandan askarawan kasar, Mohammed ben Zayed al-Nahyane a jiya alhamis

Shugaba Macron dai ya yi amfani da kyaukyawar huldar tsaro dake tsakanin kasarsa da ta Daular larabawa, wajen sabe kwangilar da aka kiyasata cewa ta kai ta Euro biliyan daya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.