''Ana gaf da murkushe IS'' a cewar shugaba Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce nan ba da jimawa ba za a murkushe kungiyar IS musamman a kasashen Iraki da kuma Syria, to sai dai wannan ba ya nufin cewa an kawo karshen ayyukan ta’addanci a cewarsa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Macron wanda ke gabatar da jawabi ga sojojin Faransa da ke wani bariki a Abu Dhabi, ya ce sun yi nasara a kan mayakan na IS a garin Raqa, abin da ke tabbatar da cewa a cikin ‘yan watanni kadan masu zuwa za a murkushe kungiyar baki daya ta fannin soji.
To sai dai shugaban na Faransa ya bayyana cewa bayan murkushe kungiyar ta hanyar amfani da soji, mataki na gaba shi ne tabbatar da cikakken tsaro, abin da ya ce yana daukar dogon lokaci.
Barikin sojin Abu Dhabi, shi ne daya tilo da Faransa ta mallaka a wata kasa baya ga nahiyar Afirka, kuma an bude shi ne bayan kammala yakin tekun Pasha (1990-1991).
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu