Isa ga babban shafi
Catalonia

Korarren shugaban Catalonia ya mika kansa

Korarren shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont, tare da wasu tsaffin minsitocinsa 4, sun mika kansu ga jami'an tsaron kasar Belguim, inda suke gudun hijira.

Korarren shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont yayinda yake halartar taro da manema labarai a birnin Brussels na Belgium.
Korarren shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont yayinda yake halartar taro da manema labarai a birnin Brussels na Belgium. REUTERS/Yves Herman
Talla

A ranar Juma’a wata babbar kotu a Spain ta bada umarnin a kamo mata Puigdemont, bayan kin bayyana da ya yi a gabanta, domin amsa tambayoyi kan rawar da ya taka kan fafutukar ballewar yankin daga kasar, duk da haramcin kotu kan yunkurin.

Tun a ranar Litinin Puigdemont da tsaffin ministocinsa 4, suka tsere zuwa Belgium, bayan da gwamnatin Spain ta rushe shugabancinsa na yankin Catalonia da ke amfana da wani mizani na cin gashin kai, tare da rushe majalisar yankin.

Tun daga waccan lokacin ne kuma Spain ta fara mulkar yankin kai tsaye, tare da tsaida ranar 21 ga watan Disamba a matsayin ranar da za’a yi sabon zaben shugabanci da na majalisar dokokin yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.