Iyalan Merah sun soki hukuncin kotun Faransa
Kotu a Faransa ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 a kan Abdelkader Merah, dan uwan Mohamed Merah, wanda ya kai hari tare da kashe mutane 7 cikin har da Yahudawa uku a shekara ta 2012 a Faransa.
Wallafawa ranar:
Masu gabatar da kara a kasar ta Faransa sun bayyana rashin gamsuwar su da hukuncin da aka yankewa dan’uwan Abdelkader Merrah.
Alkalan kotun sun yankewa Fettah Malki hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari saboda shiga haramtattun kungiyoyi amma ba wai yana da hannu wajen kai harin ba.
Lauyan Merah, Eric Dupont Morreti ya bayyana rashin gamsuwar sa dangane da wannan hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu