Isa ga babban shafi
Faransa

Wutar daji ta yi mummunan ta'adi a Faransa

Wutar daji ta yi mummunan ta’adi a yankin Corse da ke Faransa, inda zuwa safiyar yau litinin ta lalata filin da fadinsa ya kai kadada dubu 2.

Wani jirgin saman kashe gobara a yankin Carros.
Wani jirgin saman kashe gobara a yankin Carros. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Wutar ta fara ne a ranar lahadin da ta gabata, daga wani gari mai suna  Ville-du-Paraso, kuma kafin safiyar litinin ta yadu zuwa sauran yankuna, lamarin da ya tilasta wa hukumomi aikewa da jami’an kwana-kwana domin kashe gobarar.

Yanzu haka an tura dimbin jami’an kashe gobara, da jiragen sama masu feshin ruwa da sauran kayan aiki domin rage karfin wutar dajin, tare da fara aikin kwashe daga yankunan da ake ganin cewa suna da hatsari sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.