Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar dokokin Faransa ta amince da sabuwar dokar yaki da ta’addanci

Majalisar dokokin Faransa ta amince da sabuwar dokar yaki da ta’addanci da gwamnatin Emmanuel Macron ta gabatar, sakamakon yadda kasar ke ci gaba da fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda a wannan zamani.

Wasu 'yan sandan kasar Faransa da ke aiki a karkashin sashi na musamman na yaki da ta'addanci, yayinda suke sintiri a arewacin Faransa.
Wasu 'yan sandan kasar Faransa da ke aiki a karkashin sashi na musamman na yaki da ta'addanci, yayinda suke sintiri a arewacin Faransa. DENIS CHARLET / AFP
Talla

Sabuwar dokar wadda za ta maye gurbin dokar ta bacin da aka kafa bayan mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa birnin Paris a shekara ta 2015, ta samu gagarumin rinjaye daga ‘yan majalisar, duk da cewa kungiyoyin fararen hula da masu fafutukar kare hakkin bil’adama sun nuna rashin amincewarsu da ita.

Masu adawa da dokar na zargin aiwatar da ita, zai kasance wata dama ga jami’an tsaron kasar domin cin zarafin jama’a da kuma tauye hakkokinsu.

Dokar dai ta bai wa jami’an tsaron Faransa karin karfi na kai samame gidajen jama’a, da kuma tsare mutum na tsawon kwanaki ba tare da an gurfanar da shi gaban alkali ba.

Har ila yau sabuwar dokar na bai wa gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi damar tasa keyar wanda ake zargi da ta’addanci ba tare da an samu umurnin hakan daga alkali ko kuma wata kotu ba, lamarin da wasu ke ganin cewa shakka babu, dokar za ta iya haddasa tarnaki ga irin ‘yancin da jama’a ke da shi a kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.