Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ana jan kafa kan bukatun ficewar Birtaniya a kungiyar Turai

A taron shugabannin kasashen Tarayyar Turai da aka soma na kwanaki biyu a yau Alhamis, Firaministan Birtaniya Theresa May ta bukaci shugabannin su gaggauta fito da tsarin tattaunawa ficewar kasar daga kungiyar musamman kan makomar ‘yan kasashen Turai da ke Birtaniya.

Firaministan Birtaniya Theresa May tare da shugabannin Tarayyar Turai da suka hada da  shugaban Faransa Emmanuel Macron
Firaministan Birtaniya Theresa May tare da shugabannin Tarayyar Turai da suka hada da shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Yves Herman
Talla

Wannan na zuwa a yayin da shugabanin ke shirin jinkirta tattaunawar kasuwanci tsakaninsu da Birtaniya har zuwa watan Disemba.

A lokacin da ta isa taron shugabannin na Turai, Theresa May ta fadi cewa sauran takwarorinta 27 a kungiyar yana da wahala su amince an samu ci gaba a tattaunawar ficewar Birtaniya wanda zai bayar da damar shiga mataki na biyu na tattaunawar.

May ta shaidawa taron shugabannin cewa su fara shirin tattauna batun kasuwanci a taron watan Disemba da za a yi da kuma sauran yarjeniyoyin da suka shafi ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

Gabanin taron dai, a wani mataki na jan ra’ayin shugabannin Turai, Firaministar ta wallafa wata budaddiyar wasika ga ‘yan kasashen Turai sama da miliyan 3 da ke zaune a Birtaniya cewa gwamnatinta za ta kula da su ba tare da nuna banbanci ba.

Sannan ba za a tursasa ma su ficewa ksasar ba bayan Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai a watan Maris na 2019.

Muhimman bukatun da Tarayyar Turai ke son Birtaniya ta aminta da su sun hada da kudaden da kasar za ta biya na ficewa daga kungiyar da makomar ‘yan kasashen Turai a Birtaniya da kuma Arewacin Ireland.

A gobe juma’a ake sa ran shugabannin Tarayyar Turai za su tattauna batun ficewar Birtaniya amma ba tare da Firaministar kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.