Isa ga babban shafi
Jamus

Angela Markel na neman hadin kan Jam'iyyun Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara wata tattaunawar neman hadin-kan jam’iyyun kasar don kafa gwamnatin hadaka. Matakin tattaunawar ya biyo bayan koma bayar da Merkel ta fuskanta sakamakon babban zaben kasar da ya  gudana ranar 24 ga watan Satumban da ya gabata.

Matukar dai Angela Merkel ta gaza samun hadin kan jam'iyyun siyasar Jamus, hakan manuniya ce ga yiwuwar ga yiwuwar sake gudanar da zabe a zagaye na biyu.
Matukar dai Angela Merkel ta gaza samun hadin kan jam'iyyun siyasar Jamus, hakan manuniya ce ga yiwuwar ga yiwuwar sake gudanar da zabe a zagaye na biyu. REUTERS/Matthias Rietschel
Talla

Merkel, wadda ta yi nasara a ranar 24 ga watan daya gabata amma ba tare da samun gagarumin rinjaye ba,sakamakon ya nuna koma bayan siyasar da jam’iyyarta ta samu, hakan kuma yasa dole ta bukaci tattaunawa da manyan jam’iyyun kasar.

Tattaunawar ta yau na gudana tsakanin Merkel da Jam’iyyun Liberal da na FDP yayinda kuma ta tsara tattaunawa da jam’iyyar Green nan gaba kadan.

Don gujewa sake gudanar da wani sabon zaben a nan gaba, dukkanin jam’iyyun sai sun amince da kudure-kudiren da za ta gabatar musu da suka kunshi batun ‘yan cirani da kungiyar tarayyar Turai da kuma yarjejeniyar yanayi.

Matukar dai tattaunawar ta yau ta tafi yadda ya kamata, dukkanin jam’iyyun za su sake haduwa a Juma’a mai zuwa don kulla yarjejeniyar da zata kai ga kafa gwamnati cikin watan Janairu mai zuwa.

Wannan dai shi ne karon farko da za a gudanar da gwamnatin hadaka a matakin kasa baki daya a Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.