Isa ga babban shafi
Spain-Calatonia

Kotu ta soke zaben raba gardamar Catalonia

Kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasa a Spain ta soke dokar da ta bai wa Catalonia damar shirya zaben raba gardamar neman cikaken ‘yancin kai. Hukunci da ke zuwa a dai-dai lokacin da Dubban al’ummar Catalonia ke boren kame Manyan shugabanni ‘yan aware, ya sake harzuka tashin hankali a kasar.

Mutane Catalonia na zanga-zanga
Mutane Catalonia na zanga-zanga REUTERS/Juan Medina
Talla

Ma'aikata a Barcelona da sauran birane Spain sun yi jerin gwano a kan tittuna bayan kotun Madrid ta aike Jordi Cuixart da Joredi Sanchez gidan yari kan zargin ingiza rikici.

Masu zanga-zanga da ke ambatar ‘tursawa ba shine masalaha ba’, sun yi cun-curundo a gini ofishin gwamnatin yankin Catalan da ke tsakiyar Barcelona.

Carme Guell mai shekaru 62, da itama ta shiga gangami, ta ce wannan yunkuri na nufi za a iya aike kowa gidan yari, bayan mulkin mallaka da ake wa yankin.

Aike Mutun biyu gidan yari na zuwa ne adai-dai lokacin da kasar ke sake rincabewa da rikicin siyasar da ta fada ciki, irinsa mafi girma tun dawowarta salon mulkin demokuradiya a shekara ta 1977.

Wasu alkallumar da aka fitar yau sun nuna cewa kusan manyan kamfanoni 700 da ke Catalonia sun dauke hedikwatarsu daga yankin.

Kazalika birnin Madrid ya sanar da cewa zai rage hasashen habbakan sa na shekara mai zuwa daga maki 2.6 zuwa maki 2.3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.