Isa ga babban shafi
Spain

'Yan Catalonia sun matsa lamba ga Carles Puidgemont

Wasu taron al’ummar Catalonia sun ce a shirye su ke su gudanar da wani gangami kan manyan titunan yankin don matsa lamba ga shugaba Carles Puidgemont game da batun samun ‘yancin yankin a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga al'ummar yankin kan bukatarsu ta ballewa.
Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga al'ummar yankin kan bukatarsu ta ballewa. Fuente: Reuters.
Talla

Taron da ya kunshi Malaman makarantu da dalibai da iyaye, wadanda tun da farko su ne su ka yi tsayuwar daka ranar daya ga Oktoba don ganin an samu nasarar kada kuri’ar raba gardamar ballewar yankin, na ci gaba da nuna goyon bayansu ga bukatar ballewar tare da nuna kin amincewa da sabbin matakan da ake dauka don tattaunawa da gwamnatin Spain.

Yanzu haka dai Carles na fuskantar Kalubale a dai dai lokacin da ya rage kwana guda wa’adin daya dauka tun da farko na sanar da ‘yancin yankin a matsayin kasa mai cin gashin kanta ya cika.

A bangare guda dai Carles na fuskantar barazana daga manyan kasashen duniya da kungiyar tarayyar Turai na mayar da shi saniyar ware matukar ya ci gaba da daukar matakin ayyana yankin a matsayin kasa mai cin gashin kai

Haka zalika gwamnatin Spain ta yi barazanar kwace 'yancin yankin ta yadda za a ika mulkarsu daga Madrid sabanin yadda su ke gudanar da harkokin mulkinsu yanzu a Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.