Ana zargin manyan jami'an ma'aikatar tsaro da rashawa
Masu bincike a ma’aikatar shari’a ta Faransa na zargin wasu jami’an ma’aikatar tsaron kasar da rashawa wajen bayar da hanyar jiragen saman dakon jiragen yakinta zuwa waje.
Wallafawa ranar:
Tuni masu bincike suka kai samame a sashen da ke kula da ajiyar kayayyaki na ma’aikatar tsaron da ke Villacoublay kusa da birnin Paris, inda suka gudanar da bincike.
Jaridar Le Monde da ake bugawa a kasar ta ruwaito cewa ma’aikatar tsaron na bayar da hayar jiragen a kan kudaden da suka kama daga Euro milyan 50 zuwa milyan 60 kowace shekara a daidai lokacin da sojojin kasar ke fama da rashin jiragen da za su yi jigilarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu