Isa ga babban shafi
EU-Faransa

Wasu 'yan adawa na son a cire tutar EU a Faransa

Wani batu da ya janyo cece-kuce a Faransa shi ne batun kasancewar tutar Tarayyar Turai a majalisar kasar, inda wasu ‘yan adawa suka bukaci a cire Turar, yayin da kuma shugaba Emmanuel Macron ya yi watsi da bukatar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Ludovic Marin/Pool
Talla

'Ya'yan jam’iyyar Jean-Luc Melenchon wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa kuma masu adawa da manufofin Tarayyar Turai ne suka bukaci a cire Tutar daga zauren karamar Majalisar kasar.

‘Yan adawar na gani tutar mai launin bula da doruwa tamkar karan tsaye ne ga manufofinsu bayan shafe sama da shekaru 10 ana ajiye Tutar kusa da Tutar Faransa a Majalisar.

Bukatar cire Tutar kuma ya samu karbuwa daga ‘ya'yan jam’iyyar FN masu tsattsauran ra’ayi ta Marine Le pen, wacce ta kyamaci tutar a yakin neman zabenta.

‘Yan adawar dai sun bukaci a sauya Tutar da Tutar Majalisar Dinkin Duniya a Majalisar, bukatar da bangaren jam’iyya mai mulki ta Emmanuel Macron suka yi watsi da shi.

Nan gaba ne dai Macron mai ra’ayin Tarayyar turai zai sanya hannu kan wata dokar tabbatar da amincewa da Tutar wanda kuma zai tilasta daura Tutar a gine-ginen gwamnatin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.