Isa ga babban shafi
EU

Gurbacewar Iska na kashe mutane 500,000 a duk shekara

Kungiyar Kasashen Turai ta ce mutane sama da 500,000 ke mutuwa a fadin Turai kowacce shekara sakamakon shakar gurbatacciyar iska duk da kokarin da hukumomi ke yi na magance gurbacewar muhalli.

Gurbacewar Iska na Kisa a Turai
Gurbacewar Iska na Kisa a Turai CHINA OUT AFP PHOTO STR / AFP
Talla

Hukumar kula da muhalli ta kasashen Turai ta bayyana cewar mutane 520,400 ke mutuwa kowacce shekara a kasashen Turai sakamakon gurbacewar muhalli musamman abinda ya shafi hayakin man fetur da iskar gas.

Alkaluman hukumar sun nuna cewar adadin mutanen da suka mutu a shekarar 2014 ya kai 520,400 sabanin 550,000 da aka samu a shekarar 2013.

Rahotan ya ce daga cikin adadin mutane 4 cikin ko wadanne 5 sun mutu ne sakamakon shakar hayakin da ke dauke da sinadarin macrin da kan shiga huhu da kuma hanyoyin jinni.

Alkaluman sun nuna cewar kashi 82 na mazauna biranen Turai na fuskantar wannan matsala.

Kwamishinan muhalli na Turai Karmenu Vella ya ce a shirye kungiyar take ta magance matsalar da kuma taimakawa kasashen da matsalar tafi girma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.