Isa ga babban shafi
Spain-Calatonia

An yi zanga-zangar adawa da ballewar Catalonia a Spain

Dubban jama’a ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da ballewar yankin Catalonia daga kasar Spain a jiya Lahadi, a daidai lokacin da shugaban yankin Carles Puigdemont ke shirin gabatar da jawabi gaban Majalisar Dokoki a gobe Talala.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da ballewar Catalonia daga Spain
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da ballewar Catalonia daga Spain 路透社。
Talla

Zanga-zangar ta jiya ita ce irinta ta farko da masu adawa da ‘yancin yankin suka gudana a birnin Barcelona wanda shi ne babbar cibiyar masu fufutukar ballewar Catalonia, mako daya bayan kuri’ar da aka kada wadda sakamakonta ke bai wa masu wannan fata gagarumin rinjaje.

Alkaluma na nuni da cewa sama da mutane dubu 900 ne suka shiga zanga-zangar ta jiya, in da jama’a ke nuna adawa da wannan yunkuri na ballewa, yayin da wasu daga cikinsu ke yin kira da a shiga tattauna domin warware wannan rikici a siyasance.

To sai dai kwana daya kafin wannan zanga-zanga ta jiya, Firaministan Spain Mariano Rajoy, ya ce ba zai tattauna da masu neman ballewar ba har sai sun janye wannan barazana tasu, in da ya yi kashedin cewa matukar suka kuskura suka shelanta ‘yancin, to zai yi amfani da karfin ikonsa domin soke ‘yancin cin gashin-kai na yankin na Catalonia.

Zanga-zangar ta jiya Lahadi dai wani karin kwarin gwiwa ne ga mahukunta birnin Madrid, wadanda ke ci gaba da jaddada yunkurin cewa ballewar yankin na Catalonia na a matsayin wadda ya saba wa doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.