Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa na kada kuri'a kan yaki da ta'addanci

A wannan Talata ne Majalisar Dokokin Faransa za ta kada kuri’a dangane da sabuwar dokar yaki da ayyukan ta’addanci a kasar, lamarin da zai kawo karshen aiki da dokar ta baci da aka kafa tsawon shekaru biyu da suka gabata a kasar.

Majalisar Dokokin Faransa na kada kuri'a kan sabuwar dokar yaki da ta'addanci da za ta maye gurbin dokar ta baci da aka kafa bayan harin ta'addancin da kungiyar ISIS ta kai wa kasar a shekarar 2015
Majalisar Dokokin Faransa na kada kuri'a kan sabuwar dokar yaki da ta'addanci da za ta maye gurbin dokar ta baci da aka kafa bayan harin ta'addancin da kungiyar ISIS ta kai wa kasar a shekarar 2015 REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Gwamnatin Emmanuel Macron ce ta gabatar da wannan sabon daftari a gaban Majalisar, lura da yadda wasu ke kallon dokar ta bacin da ake amfani da ita a tsawon shekaru biyu da cewa tana tauye hakkokin jama’ar kasar.

Christine Lazerges, shugabar hukummar kare hakkin bil’adama a kasar ta Faransa, ta ce aiki da dokar ta bacin ya kasance wata dama ta cin zarafi da kuma tauye wa jama’a hakkokinsu a tsawon wadannan shekaru biyu.

To sai dai ministan cikin gidan kasar Gerard Collomb, ya bayyana sabuwar dokar a matsayin wadda za ta taimaka wajen rage irin barazanar da kasar ke fuskanta daga ‘yan ta’adda da kuma masu tsatsaurar akida.

An dai fara amfani da dokar ta baci a kasar ne bayan harin da kai cikin watan nuwamba a birnin Paris inda aka samu asarar rayukan sama da mutane 130.

To sai dai kuma wasu na ganin cewa irin matakan da aka cusa a cikin sabuwar dokar wadda Majalisar Dokokin ke shirin tafka mahawara akai a wannan talata, matakai ne tsaurara da za su iya kawo cikas ga ‘yancin da jama’a suke da shi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.