Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya bayyana manufofinsa akan Tarayyar Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci hadin kan kasashen Turai a wani jawabi da ya kunshi manufofinsa na kaddamar da sauye sauye a Yankin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da manyan manufofinsa akan ci gaban Tarayyar Turai
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da manyan manufofinsa akan ci gaban Tarayyar Turai REUTERS/Ludovic Marin/Pool
Talla

Shugaban ya bukaci karin hadin kai da zai zarce wanda ake da shi yanzu a bangarorin tattalin arziki da tafiyar da gwamnati da kuma bangaren tsaro.

Macron ya gabatar da manyan manufofinsa ga ci gaban Tarayyar Turai inda ya zayyana jerin sauyen-sauyen da ya ke son aiwatarwa da suka shafi tattalin arziki da tsarin siyasa da kuma daidaita dokoki a fadin Turai.

Manufofin dai sun shafi makomar Tarayyyar Turai bayan ficewar Birtaniya a kungiyar.

Manufofin Macron ga ci gaban Tarayyar Turai

Manufofin da shugaba Macron ya gabatar sun hada da tsarin samar da ministan kudi da kasafi da kuma majalisa a tsakanin mambobin Tarayyar Turai tare da kafa runduna ta musamman da za ta yi aiki tare da rundunonin kasashen kungiyar.

Sannan da samar da sabuwar rundunar ‘yan sanda da za ta kula da iyakokin ruwan Turai domin dakile kwararar baki.

Akwai kuma sabon tsarin haraji da shugaba Macron ya ke so a daidaita, daga cikin manufarsa shi ne samar da wani tsarin haraji na musamman ga kamfanonin fasaha kamar Facebook da Apple kan tasirinsu ga ci gaban kasa maimakon ribar da suke kwasa a kasashen Turai

Sannan da sabon haraji ga kamfanonin da ke gurbata muhalli a Turai

Shugaba Macron kuma na son a bullo da tsarin ba daliban kasashen Turai lakantar harshe biyu ta hanyar ba su damar kwashe watanni shida a wata kasa a nahiyar tare da bullo da tsarin muhawara tsakanin ‘yan kasshen Turai akan bukatunsu ga Tarayyar Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.