Isa ga babban shafi
Amurka

Adadin kasashen da Trump ya haramtawa shiga Amurka ya karu

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake tsawaita wa’adin aikin da dokar nan da ke hana ‘yan asalin wasu kasashen duniya shiga kasar bisa zargin cewa shigarsu kasar na iya kawo cikas ga sha’anin tsaro.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Bayan karewar wa’adin kwanaki 90 na farko, shugaba Trump ya kara adadin kasashen da haramcin ya shafa daga jiya lahadi.

Koriya ta Arewa, Venezuela da kuma Chadi, sune kasashen da aka kara karkashin dokar da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu a jiya Lahadi, yayin da aka janye Sudan daga cikin kasashe shiddan farko da suka share tsawon kwanaki 90, ana amfani da dokar a kansu.

Amurka dai ta bayyana ‘yan asalin wadannan kasashe a matsayin wadanda ke kawa cikas ga sha’anin tsaronta, ko kuma wadanda ba sa bai wa Amurka cikakken hadin-kai ta hanyar musayar bayanai da suka shafi matafiya.

Matakin aiki da dokar ya sha bambam a tsakanin kasashe, domin kuwa ilahirin ‘yan asalin kasashen Koriya da Arewa da kuma Chadi ne aka haramta wa shigar kasar ta Amurka, yayin da aka kayyade adadin wadanda matakin zai shafa daga kasar Venezuela.

Bayan cire kasar Sudan kuwa, har yanzu matakin zai ci gaba da shafar kasashen Iran, Libya, Syria, Somalia, da kuma Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.