Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya sanya hannu kan dokar kwadago

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya hannu a kan sabuwar dokar fasalta ayyukan kwadago a kasar a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ita.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reuters
Talla

Shugaba Emmanuel Macon ya sanya wa dokar hannu ne kamar yadda aka nuna a tashar talabijin ta kasar, matakin da ke matsayin cika daya daga ciikin alkawurransa da ya dauka a lokacin yakin neman zaben kasar na watan mayu.

Wannan dai doka ce da ke bai wa gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu damar sauya salon daukar ma’aikata tare da biyan ma’aikatan sauran hakkokinsu.

Macron ya ce yana mai matukar alfahari da samar da wannan doka, a daidai lokacin da kungiyoyin ma’aikata ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga da yajin aiki don nuna rashin amincewa da dokar.

Manyan kungiyoyin kwadago na kasar CFDT da kuma FO, sun share tsawon watanni uku suna tattaunawa da gwamnati kan wannan doka, inda suka tashin baram-baram ba tare da sun cimma jituwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.