Dan jarida Loup Bureau ya dawo Faransa
Yau lahadi ne dan jaridar nan bafaranshe mai suna Loup Bureau da ya share kusan kwanuki 50 a daure gidan maza a Turkiya ya samu komawa Faransa bayan da ya samu salama daga hukumomin Turkiya.
Wallafawa ranar:
Ranar 26 ga wata yuli ne yan sandan Turkiya suka kama shi a kan iyakar kasar da Iraki ya na dauke da wasu hotuna dake nuna shi da mayakan kurdawa.
Turkiya na zargin wannan dan jarida da hada kai da kungiyoyin yan ta’ada,
Salamar dan jaridar na zuwa ne yan lokuta bayan ziyarar da Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya kai a Birnin Ankara tareda ganawa da hukumomin kasar ta Turkiya..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu