Isa ga babban shafi
Birtaniya

An gano wani da ke da hannu a harin birnin London

Jami’an ‘yan sanda a birnin London sun cafke wani mutum da ake zargi da hannu a harin da aka kai kan layin dogon karkashin kasa da safiyar jiya juma’a da ya jikkata sama da mutum 22.Yanzu haka dai matashin mai shekaru 18 wanda ba a bayyana sunansa ba, na rike a hannun ofishin ‘yan sandan birnin da ke Dover yayinda kuma ake shirin yin gaba da shi zuwa babban ofishin ‘yan sanda da ke kudancin Birnin.

Galibin wadanda suka jikkata a harin na jiya da aka kaddamar kan layin dogon karkashin kasar na Parson Green an sallamesu daga asibiti face mutum uku da ke ci gaba da karbar kulawar gaggawa.
Galibin wadanda suka jikkata a harin na jiya da aka kaddamar kan layin dogon karkashin kasar na Parson Green an sallamesu daga asibiti face mutum uku da ke ci gaba da karbar kulawar gaggawa. Reuters
Talla

A cewar mataimakin kwamishinan ‘yan sandan birnin Neil Basu harin alamu ne na yunkurin ta’addanci kuma za su ci gaba da bincike baya da suka samu mutum guda da ake zargi da hannu ciki.

Sama da mutum 22 ne dai suka jikkata a harin na safiyar jiya juma’a da aka kai layin dogon karkashin kasa na Parsons Green a dai dai lokacin da mutanen ke kokarin tafiya wuraren aiki.

Sai dai bayanai sun ce kusan dukkanin wadanda suka jikkata a harin an sallamesu daga asibitocin da aka basu kulawar gaggawa face mutum uku da yanzu haka ke ci gaba da karbar kulawa a asibitin Chelsea da na Westminster.

Wani taro da kwamitin da ke bai wa gwamnatin Birtaniya shawara kan harkokin tsaro da yadda za a gano masu laifi karkashin jagorancin sakataren harkokin cikin gida Amber Rudd ya daldale da ayyana harin a matsayin na ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.