Isa ga babban shafi
Jamus

Angela Markel ta rasa kaso mai yawa daga magoya bayanta

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conservative ta shugabar gwamnatin Jamus ke da shi ya ragu, yayin da kashi daya cikin uku na al’ummar kasar suka gaza yanke shawara kan wanda za su kada wa kuri’a a zaben game-gari da za a gudanar cikin wannan watan.

Kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conservative mai ra’ayin rikau ta shuagabar gwamnatin kasar Angela Merkel ya ragu da kashi 36 cikin 100.
Kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conservative mai ra’ayin rikau ta shuagabar gwamnatin kasar Angela Merkel ya ragu da kashi 36 cikin 100. Reuters
Talla

sakamakon wannan kuri’ar ta jin ra ;ayin jama’a da aka fitar a wanann jumma’a, ya dada haifar da fargaba game da irin hadakar da za ta kai ga gaci a zaben game-gari da za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Satumba a Jamus.

Kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conservative mai ra’ayin rikau ta shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ya ragu da kashi 36 cikin 100.

Sai dai wasu na ganin hakan ba zai hana jam’iyyar samun rinjaye a Majalisar dokokin kasar ba.

Ita kuwa Babbar jam’yyar adawa ta Social Democratic Party ta samu karin magoya baya da kashi 23.

Su kuma jam ;iyyun FDP ta ‘yan Democrat da AFD ta masu adawa da bakin haure kowannesu na da kashi 10-10 wajen samun magoya baya.

Kuri’ar wadda aka fara gudanarwa daga 12 zuwa 14 ga watan Satumba ta kuma nuna cewa, har yanzu kashi 39 na Jamusawa ba su yanke shawarar wanda za su kadawa kuri’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.