Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta kaddamar da sabon atisayen soji

Rasha ta kaddamar wani sabon atisayen Soji yau alhamis tare da hadin gwiwar Belarus a gab da ofishin kungiyar tarayyar, lamarin da ake ganin tamkar tsokana ga hadakar kungiyar tsaron kasashen tekun atlantika ta NATO. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta tsakanin Rasha da kungiyar ta NATO game da rawar da take takawa kan rikicin kasar Ukrain.

Atisayen ya kunshi sama da dakarun soji dubu 13 da jiragen yaki 70 da kuma tankoki 250 da kuma jiragen ruwa na yaki guda 10.
Atisayen ya kunshi sama da dakarun soji dubu 13 da jiragen yaki 70 da kuma tankoki 250 da kuma jiragen ruwa na yaki guda 10. Reuters
Talla

Atisayen sojin da aka yiwa lakabi da Zapad-2017, rahotanni sun ce za a ci gaba da gudanar da shi har zuwa ranar 20 ga watan da muke ciki.

Haka kuma atisayen a cewar Moscow ya kunshi dakarun soji dubu 12 da 700 da kuma jiragen yaki 70 bayaga tankokin yaki 250 sai kuma jiragen yaki na ruwa guda 10 wanda kuma kowanne za a ci gaba da gwajinsu har zuwa ranar karshe ta atisayen.

Cikin wata sanarwa fara atisayen, ministan tsaron kasar ta Rasha ya ce atisyaen nada nufin kare kasar ne kawai ba wani yunkurin kai hari ko farmaki ga wata kasa ko kungiya ba, inda ya yi watsi ga batun razanin da wasu suka shiga sakamakon fara atisayen na Rasha.

Sai dai kungiyar tsaro ta NATO ta yi ikirarin cewa tabbas Rashan na boye wasu lamurra ga duniya musamman dangane da batun da ke cewa akwai kimanin mutum dubu 100 a atisayen sabanin adadin da aka sanar da kasa da dubu 13.

A cewar NATO Poland da Baltic da suka balle daga Rashan shekaru 25 na cikin kasashen da suka shiga razani ganin yadde atsayen ke gudana gab da su.

NATO ta ce hanya daya ta samun nutsuwa ga kasashen duniya shi ne Rasha ta bar boye-boye ta fito fili ta sanar da gaskiyar al’amuran da ke faruwa dama dalilin atisayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.