Lokaci ya kurewa masu kokarin gujewa guguwar Irma a Florida
Gwamnan jihar Florida, Rick Scott, ya shaidawa jama’arsa da aka bai wa umarnin ficewa, da su kaucewa kokarin bin tituna domin gujewa inda ake fargabar guguwar Irma zata aukawa, su kuma hanzarta samun mafakar da ta dace mafi kusa da su.
Wallafawa ranar:
Scott ya ce a halin yanzu lokaci ya kurewa wadanda ke kokarin kauracewa wuraren da guguwar ke tunkara ta hanyar amfani da motoci.
Sama da kashi 25 da al’ummar jihar ta Florida wato kimanin mutane miliyan 6 da dubu 500 aka bai wa umarnin ficewa daga gidajensu.
Har yanzu dai masana sun ce guguwar tana gudun kilomita 193 a sa’a guda duk da karfinta da ya ragu a jiya Asabar, a halin da ake ciki mutane 24 ne suka rasa rayukansu a dalilin wannan guguwa da ta ratso tsibiran yankin Carreabia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu