Isa ga babban shafi
Mexico

Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 30 a Mexico

Alkaluman mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar girgizar kasa a Mexico sun kai 32 kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Wasu daga cikin mutanen da girgizar kasar Mexico ta shafa
Wasu daga cikin mutanen da girgizar kasar Mexico ta shafa REUTERS/Edgard Garrido
Talla

Gwamnan jihar Oaxaca da ke kudancin Mexico, Alejandro Murat ya shaida wa wata kafar talabijin ta kasar cewa, mutane 17 daga cikin 32 da suka mutu ‘yan asalin garin Juchitan ne, in da gidaje da dama suka rufta da jama’a sakamakon girgizar kasar.

An kuma samu asarar rayukan mutane 7 a jihar Chiapas da ke makwabtaka da Oaxaca, yayin da hukumomin kasar ke cewa, akwai yiwuwar adadin mutanen ya haura nan gaba.

Kananan yara na cikin wadanda ibtila’in ya shafa musamman a jihar Tabasco.

Har ila yau girgizar kasar ta shafi yankin tekun Pacific da ke da tazarar kilimota 100 daga birnin Tonala na Chiapas.

Girgizar kasar mai karfin maki 8.2, ita ce mafi muni da ta afka wa Mexico tun shekarar 1985, in da aka samu irinta mai karfin maki 8.1 kuma kimanin mutane dubu 10 ne suka mutu a wancan lokaci.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake fargabar cewa, guguwar Irma da ta afka wa kasashen yakin Caribbean za ta shafi jihar Florida da wasu jihohi masu mkawbtaka da ita a Amurka.

Ana ganin ibtila’in na Irma zai tilasta wa mutane sama da dubu 100 ficewa daga gidajensu a Florida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.