Colombia: Kungiyar 'yan tawayen FARC ta rikide zuwa jami'yya
Tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen kasar Colombia mafi karfi wato FARC, da ta shafe shekaru 50, tana fafata yaki da sojin kasar, ta rikide zuwa jam’iyyar siyasa.
Wallafawa ranar:
Kwamandan kungiyar, Rodrigo Londono ne ya sanar da haka, yayin da yake jawabi ga dubban magoya bayansu a birnin Bogota, inda ya ce a halin yanzu, kungiyar ta FARC ta canza alamarta daga hotunan bindigogi zuwa hoton jajayen furanni, sai dai har yanzu jami’yyar zata cigaba da amsa sunan FARC.
To sai dai masu sharhi kan siyasa, na ganin kungiyar ta FARC na da jan aiki a gabanta, na neman jan ra’ayoyin ‘yan kasar, bayan daukar matakin na juyewa zuwa jam’iyya daga kungiyar ‘yan tawaye, kasancewar wata kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar, ta nuna cewa akalla ‘yan kasar kashi 70% sun ce ba zasu kada mata kuri’a ba.
An dauki tsawon lokaci ana tafka muhawara tsakanin bangarorin 'yan kasar ta Colombia bisa cancantar afuwar da gwamnati ta yiwa mayakan tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta FARC tare da manyan kwamandojinsu, bayan ajiye makaman da suka yi, sakamakon cimma yarjejeniyar kawo karshen fadan da suka shafe shekaru suna gwabzawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu