Isa ga babban shafi
Birtaniya

An samu raguwar marasa aiki a Burtaniya

Wasu bayanai da hukumomi a Burtaniya suka fitar yau Laraba ya nuna yadda adadin marasa aikin yi a kasar ya yi matukar raguwa kwatankwacin na shekaru 42 da suka gabata, a dai dai lokacin da kokonton ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai ke kara bunkasa daukar ma’aikatan wucin gadi.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May Reuters
Talla

Rahoton ofishin kididdiga na kasar ONS ya nuna yadda adadin yawan marasa aikin ya ragu da kimanin kaso 4.4 cikin watanni uku daga watan Yunin daya gabata lamarin da ya bayar da adadi mafi karanci na marasa aikin yi a kasar tun bayan shekarar 1975.

A cewar Ofishin, a karshen watan Yunin daya gabata, an kiyasta kimanin mutum milyan 1 da dubu dari hudu da tamanin a matsayin marasa aikin yi Burtaniyar, wanda ya haura na shekarar baya da mutum dubu dari da 57.

Daga watan Yunin,  adadin masu aikin yin ya karu da mutum dubu dari biyu da 25 inda ya kai mutum milyan 32 da digo bakwai a cewar ofishin kula da masu aiki a Burtaniyar.

Shugaban sashen kula da Ma’aikata David Morel ya ce duk da cewa akwai tantama a zukatan ma’aikatan musamman kan ficewar Burtaniyar daga kungiyar tarayyar Turai babu shakka mutane da dama sun samu ayyukan yi a ‘yan watannin baya-bayan nan wanda kuma ke da alaka da batun ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.