Isa ga babban shafi

Faransa na tattaunawa kan gurbataccen kwan da ya watsu a Turai

Majalisar dokokin Faransa ta fara tattaunawa kan gurbataccen kwan da ya watsu a nahiyar Turai mai dauke da Sinadarin Fipronil da ke da illah ga lafiyar Bil’adama.Tuni dai ta fara musayar bayanai da kuma jin ra’ayoyin bangarori daban-daban dangane da matakan da za a dauka kan kwan wanda ya fito daga kasar Netherland.

Ana ci gaba da kwashe miliyoyin kwayaye masu dauke da sinadarin guba a Faransa don kare lafiyar Al'umma
Ana ci gaba da kwashe miliyoyin kwayaye masu dauke da sinadarin guba a Faransa don kare lafiyar Al'umma REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Ministan Albarkatun gona a Faransar Stephane Travert ya shaidawa majalisar kasar da ke tattaunawa kan batun cewa akwai bukatar gaggauta samun Karin haske sosai baya ga musayar bayanai tsakanin kasashen don sanin matakin da za a dauka a gaba.

Ya zuwa yanzu dai shi wannan gurbataccen kwai da aka gaurayashi da maganin kashe kwari mai illa ga bin'adama, an same shi a kasashen Jamus, Belgium Sweden, Switzerland da Britania da kuma Faransa, yayin da kuma ake ci gaba da janye shi daga wuraren saidawa don kare lafiyar al'umma.

Ma'aikatar albarkatun gona a Faransa dai na cewa an sanar da kafa hukumar bincike domin domin gano irin barnar da gurbataccen kwan yayi.

Tuni ministan Albarkatun gona na Belgium Dennis Ducarme ya zargi hukumomin kasar Dutch da kin shaidawa kasashe’yan uwanta game da gano wannan kwai akan  lokaci, kasancewar tun watan Nuwamba na shekarar data gabata ta gano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.