Isa ga babban shafi
Ingila

Ma'aikatan bankin Ingila na yajin aikin farko cikin shekaru 50

A karon farko cikin shekaru 50, ma’aikatan babban bankin Ingila sun shiga yajin-aikin kwanaki uku, a wani mataki na neman karin albashi.

Ma'aikatan babban bankin Ingila rufe da fuskokinsu da hoton gwamnan bankin Mark Carney a yayin boren neman karin albashi a  birnin London
Ma'aikatan babban bankin Ingila rufe da fuskokinsu da hoton gwamnan bankin Mark Carney a yayin boren neman karin albashi a birnin London REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Ma’aikatan babban bankin Ingila, BoE sun yi bore a harabar bankin da ke birnin London a wannan Litinin kuma a gaban Ministan kudade John McDonnell na jam’iyyar Labor mai adawa.

Ma’aiktan da ke aiki a sassa daban daban na bankin, sun rufe fuskokinsu da wani abun rufe fuska mai dauke da hoton gwamnan bankin, Mark Carney.

Kazalika masu boren na rike da wata alama dauke da gajeren rubutun da ke cewa, ma’aikatan bankin na BoE sun cancanci albashi na kwarai.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, ma’aikatan sun bayyana bacin ransu kan yadda ake biyan su albashin da ya yi kasa da ma’aunin tsadar kayayyaki a kasar.

Sannan kuma sun bayyana fargaban cewa, babu alamar yi wa akasarinsu karin albashi a cikin wannan shekara.

Yajin aikin na kwanaki uku ya gurguntar da ayyuakan bankin na Ingila.

Ko da dai, mai magana da yawun bankin ya ce, sun yi tanadi na musamman don ganin cewa wasu sassa masu muhimmanci a bankin sun ci gaba da aiki a yayin yajin aikin.

Tuni dai BoE ya shiga tattaunawar sulhu da ma’aikatan kamar yadda mai magana da yawun ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.