Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Ana rige-rigen karbe hukumomin Tarayyar Turai daga Birtaniya

Mambobin kungiyar kasashen Turai na rige-rigen mika bukatar samun daman tafiyar da Hukumomin manyan bankunan kungiyar da na kiwon lafiya a kasarsu, yayin da wa’adin da aka bayar na kokarin sauya hukumomin ke cika.

Firaministan Birtaniya Theresa May
Firaministan Birtaniya Theresa May REUTERS/Eric Vidal
Talla

Tarayyar Turai na kokarin sauya hukumominta da ke Birtaniya matsuguni bayan ficewar kasar daga kungiyar.

A watan Nuwamba za a bayyana Sunayen biranen da suka samu nasara daukar nauyin Hukumomin biyu, wadanda ke da dubban ma’aikata.

Biranen da suka shiga takarar samun daman kafa Hukumar lafiyar ta Turai, sun hada da Amsterdam da Copenhagen da Helsinki da Lille, sai kuma Stockholm da Barcelona. kuma duk wanda ya samu wannan dama zai dibi ma’aikata 900.

Birnin Frankfurt na Jamus shi ne a kan gaba wajen daukan nauyin hukumar bankunan Turai, haka kuma Luxembourg da Paris da Prague sun shiga takarar da zai samarwa mutane 190 aikin yi.

Biranen Vienna da Dublin da Warsaw na cikin wadanda ke neman bukatar karbar hukumomin na Turai.

Shugabanni kasashen na EU 27 da suka rage sun amince a wani taro cikin watan Yuni na bin tsarin zaben sabon wurin da hukumomin zas u koma.

Shugaban Kungiyar Donald Tusk ya ce gasar da kasashen suka shiga a wannan lokacin kan wadanan hukumomin ya nuna cewa sauran kasashen 27 kansu a hade ya ke.

Tun a 1995 aka kafa hukumar kiwon lafiya ta Turai a birnin London, yayin da Hukumar bankunan Turai kuma aka kafa ta a 2011 a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.