Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

An soma tattaunawar ficewar Birtaniya a Brussels

Jakadun Birtaniya da na kungiyar Kasashen Turai sun fara cikakkiyar tattaunawar ficewar kasar, yayin da bangarorin biyu ke cewa, lokaci ya yi da za su cimma matsaya kan batutuwa da dama.

Wakilin Tarayyar Turai Michel Barnier da Ministan Birtaniya David Davis, suna tattauna batun ficewar kasar a Brussels
Wakilin Tarayyar Turai Michel Barnier da Ministan Birtaniya David Davis, suna tattauna batun ficewar kasar a Brussels REUTERS/Francois Lenoir
Talla

A wannan Litinin din ne Birtaniya da kungiyar kasashen Turai suka fara cikakkiyar tattaunawa game da ficewar kasar a birnin Brussels.

Ministan Birtaniya kan ficewar kasar daga Tarayyar Turai wanda kuma ke matukar nuna adawa ga kungiyar, David Davis ya ce, lokaci ya yi da za su cimma matsaya a wanann tattaunawa ta kwanaki hudu.

Sai dai a yayin da aka shiga tattaunawar, jaridun Birtnaiya sun mayar da hankali ne kan rarrabuwar kawunan da aka samu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar Conservative mai mulki a lokacin zaben raba gardama na ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Sannan Firaminista Theresa May da ta rasa rinjaye a Majalisar Dokoki a zaben da aka gudanar a watan jiya, na shan tambayoyi daga Jam’iyyar game da karfin ikon da ta ke da shi a yanzu, abin da jakadun na tarayyar Turai ke kallo a matsayin damuwa.

Makomar ‘yan kasashen Turai da ke rayuwa a Birtaniya da kuma na Birtaniya da ke rauyuwa a kasashen Turai da zancen kasuwanci tsakanin bangarorin biyu da batun iyakar Ireland na daga cikin abubuwan da za su tattauna.

Nan da watanni 20 masu zuwa ne, ake sa ran kammala ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.