Isa ga babban shafi
Birtaniya-Saudiya

Kotun Birtaniya ta ce kasar nada ‘yancin sayarwa Saudiya makamai

Wata Babbar kotun Birtaniya ta ce gwamnatin kasar nada ‘yancin sayarwa Saudiya da makamai a yakin da ta ke jagoranta a Yemen. An shigar da karar ne kan yadda Saudiya ke kashe fararen hula da sunan yakar ‘Yan tawayen Huthi.

Birtaniya ke sayarwa Saudiya da makamai a yakin da ta ke jagoranta a Yemen.
Birtaniya ke sayarwa Saudiya da makamai a yakin da ta ke jagoranta a Yemen. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Masu fafutikar da suka shigar da karar sun ce za su kalubalanci hukuncin na kotun.

Kotun ta yi watsi ne da karar da aka shigar gabanta kan zargin gwamnatin Birtaniya da saba doka kan rashin dakatar da sayarwa Saudiya da makamai a yakin da ta ke jagoranta a Yemen.

Wata kungiya mai fafutika kan adawa da cinikin makamai ta shigar da karar inda Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren sama da Saudiya da kawayenta ke kai wa akan ‘yan tawayen Huthi ‘yan Shi’a sun yi sanadin mutuwar dubban fararen hula.

Makaman da Birtaniya ke sayarwa Saduiya sun hada da jiragen yaki da bama bamai.

Kotun ta ce babu wata doka da gwamnatin Birtaniya ta saba na Sayarwa saudiya da makaman.

Amma Kungiyar da ta shigar da karar ta yi allawadai da hukuncin tare sha alwashin daukaka kara domin kalubalantar hulkuncin kotun

Tun a 2014 Saudiya da kawayenta kasashen larabawa 6 suka kaddamar da farmaki akan ‘yan tawayen Huthi a Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.