Isa ga babban shafi
Turai

Ministocin Jamus, Faransa da Italiya na taro kan bakin haure

Ministocin cikin gida na kasashen Jamus Faransa da kuma Italiya sun tattaunawa a birnin Paris kan yadda zasu magance karuwar tudadar bakin haure zuwa nahiyar turai.

Wasu bakin haure da jami'an agaji suka ceto daga tekun Meditarranean
Wasu bakin haure da jami'an agaji suka ceto daga tekun Meditarranean
Talla

Taron na a matsayin sharar fagega wanda kungiyar tarayyar turai EU zata jagoranci, ‘ya’yanta cikin kasa da kwanaki 7, kasar Estonia.

A satin da ya gabata ne Italiya tayi barazanar rufe tashoshin jiragen ruwanta, tare da datse duka wani jirgi mai dauke da bakin haure daga Libya da kungiyoyin agaji suka ceto daga tekun Meditarranean, muddin sauran kasashen turai basu agaza mata wajen daukar nauyin ‘yan gudun hijirar ba, wadanda a wannan shekarar sama da 80,000 ne suka ketara cikin kasar.

Sama da bankin haure 500, 000 ne suka ketara takun na Meditarranean zuwa kasar Italiya, daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Daga farkon shekara 2017 da muke ciki zuwa yanzu kadai kuma sama da bakin hauren 83,650 suka ketara zuwa Italiya; Karin kashi 20 a kan na shekarar 2016 da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.