Isa ga babban shafi
Jamus

Majalisar Jamus ta amince da dokar auren jinsi guda

Majalisar dokokin Jamus ta kada kuri’ar amincewa da kudirin auren jinsi guda a yau Juma’a, wanda ya sabawa zabin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da ke adawa da auren jinsi.

Zauren Majalisar dokokin Jamus a Berlin
Zauren Majalisar dokokin Jamus a Berlin REUTERS
Talla

Kudirin ya samu amincewar ‘Yan majalisa 393 akan 226 da suka kada kuri’ar kin amincewa. Tuni kudirin ya samu amincewar majalisar dattijai.

Dokar auren jinsin kuma ta bayar da dama ga ‘Yan luwadi da madigo su mallaki ‘ya’ya, daga gidan marayu.

Cikin ‘yan majalisar da suka amince da kudirin har da mambobin jam’iyar Angela Merkel duk da tana adawa da matakin.

Merkel ta ba ‘Yan Jam’iyyarta damar bin ra’ayinsu maimakon bin ra’ayin jam’iyya.

Jam’iyyar  Angela Merkel ta share tsawon shekaru tana adama da samar da wannan doka.

Kasar Jamus ta kasance daya daga cikin kasashen yammacin duniya da dama a yanzu da suka amince da wannan doka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.