Isa ga babban shafi
Birtaniya- EU

‘Yan kasashen Turai za su ci gaba da zama a Birtaniya

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta ce ko bayan ficewar kasar daga Kungiyar Turai, ‘yan asalin kasashen yankin na da damar ci gaba da rayuwar a kasar har na tsawon shekaru biyar domin kintsawa. Kasashen na Turai sun yaba da wannan mataki na Firaminista May. 

Firaministan Birtaniya Theresa May da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Firaministan Birtaniya Theresa May da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel REUTERS
Talla

Theresa May, wanda ke gabatar da jawabi lokacin wata liyafar cin abincin dare tare da shugabannin yankin na Turai, ta ce makomar ‘yan asalin kasashen da ke zaune a Birtaniya bayan janyewar kasar daga Tarayyar Turai, na daga cikin muhimman batutuwa uku da ke gaban gwamnatinta.

Ta ce ba wani dan asalin wadannan kasashe da za a bukaci ya fice daga kasar bayan kammala janyewar har tsawon shekaru biyar da za su biyo baya.

Wannan dai ya kara kwantar da hankula a daidai lokacin da ake fargaba dangane da makomar milyoyin ‘yan asalin kasashen na Turai da ke zaune a Birtaniya bayan raba-gari a tsakanin bangarorin biyu.

Shugabar gwmanatin Jamus Angela Merkel, ta ce wannan mataki ne mai kyau, duk da cewa suna bukatar karin bayani daga Theresa May dangane da wannan batu.

Wasu daga cikin batutuwan da aka cimma matsaya a tattanaunawar da aka fara tsakanin bangarorin biyu a halin yanzu, sun hada da tsayar da watan Nuwamba mai zuwa domin zaben sabbin birane da za su karbi manyan cibiyoyin Kungiyar da za a dauke daga Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.