Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya sake fasalta dokar yaki da ta’addanci a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana sabuwar dokar yaki da ayyukan ta’addanci da gwamnatinsa ta yi wa kwaskwarima, wadda tuni ta ke fuskantar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan’adam.

Emmanuel Macron, shugaban Faransa
Emmanuel Macron, shugaban Faransa REUTERS
Talla

Shugaban ya gabatar da dokar a taron ministocinsa wacce aka sake fasalta tsarinta da za ta bada damar tsawaita aiki da dokar ta-bacin da aka kafa tun a watan Nuwamban 2015.

Sau biyar ana kara wa’adin dokar ta-bacin da aka kafa a kasar bayan mutuwar mutane 130 a hare haren da aka kai a Paris.

A tsakiyar Yuli wa’adin dokar zai kawo karshe, kuma ana tunanin shugaba Macron zai tsawaita dokar zuwa watan Nuwamba kafin tabbatar da sabuwar dokar yakar ta’addanci da aka yi wa kwaskwarima.

Tuni dai babbar kotun Faransa ta bai wa majalisar kasar damar fara nazari kan tsara sabuwar dokar duk da kungiyoyin kare hakkin biladama na bayyana fargaba kan yadda dokar za ta ba wa jami’an tsaron kasar karfi fiye da kima wajen aiwatar da ita.

Amnesty international ta koka kan yadda hukumomin tsaron Faransa ke amfani da dokar ta-baci, wajen hana al’umma gudanar da zanga zangar da dokar kasa ta basu dama.

Abin da sabuwar dokar ta kunsa.

Sabuwar dokar, ta ba mahukuntan Faransa ‘yancin kula da tsaron wani babban taro ko wani wurin da ke fuskantar barazanar hari ba tare da neman izinin kotu ba.

Sannan dokar ta ba jami’an tsaro, ‘yancin gudanar da binciken kwa-kwaf ba tare da neman izinin wani ba.

Dokar ba bayar da izinin rufe duk wani wajen ibada na tsawon watanni shida da ke yada fatawar tsattsauran ra’ayi.

Sannan izinin mallakar bindiga ya koma hannun gwamnatin Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.