Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya fuskanci turjiya daga shugabannin gabashin Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya fuskanci turjiya daga shugabannin kasashen gabashin Turai, a kan kudirinsa na sauya tsarin daukar ma’aikatan kwadago daga mambobin kungiyar Tarayyar Turai.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel, sai kuma Fira ministan Birtaniya Theresa May, a birnin Brussels, yayin taron kungiyar kasashen nahiyar turai, a ranar 22 ga watan Yuni shekarar 2017.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel, sai kuma Fira ministan Birtaniya Theresa May, a birnin Brussels, yayin taron kungiyar kasashen nahiyar turai, a ranar 22 ga watan Yuni shekarar 2017. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Shugabannin kasashen, sun yi kira ga shugaba Macron ya jingine bukatar wacce aka shafe shekaru 20 ana cin moriyar tsarin tsakanin kasashen Tarayyar Turai.

Shugaba Macron dai na ganin kasashen na gabashin Turai sun mamaye ayyukan yi a Faransa, kamar yadda ta faru a Birtaniya, wadda yake daya daga cikin dalilan da ya sanya kasar ta balle daga kungiyar tarayyar turai.

Shugaban na Faransa, na son sauya tsohon tsarin kwadagon na Tarayyar Turai, wanda aka ba kamfanoni damar bai wa kwararru aiki daga mambobin kungiyar.

Kasashen na gabashin Turai, suna kallon matakin na shugaban Macron tamkar cin fuska a gare su.

To sai dai kasashen da suka hada da Poland da takwarorinta na Hungary, Jamhuriyyar Czech da Slovakia sun amince da bukatar zaunawa a fahimci juna kan banbancin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.