Isa ga babban shafi
Portugal

Jami'an tsaron Portugal sun taka rawa wajen konewar mutane

Fira Ministan kasar Portugal Antonio Costa ya nemi jami’an tsaron kasar da su bayyana wa duniya dalilan da suka sanyasu datsewa mutane hanyar tserewa daga mahaukaciyar wutar dajin da ta ke cigaba da tafka barna a kasar wadda ya zuwa yanzu ta lakume rayukan mutane 64.

Wutar dajin da ke cigaba da barna a kasar Portugal.
Wutar dajin da ke cigaba da barna a kasar Portugal. PAULO NOVAIS/LUSA
Talla

Wannan na zuwa ne a wani lokaci da wani jirgin sama da ke feshin ruwan kashe gobaran ya rikito.

PM kasar ya tilas jami’an tsaron kasar su yi cikakken bayani, kan makasudin da yasa suka ki barin masu ababan hawa dake kaucewa gobarar bin wata hanya daban inda babu hatsari, inda suka rika iza keyar masu ababan hawa bi ta hanyar da gobarar ke ci har aka sami hasarar rayukan mutane 64.

An dai gano cewa mutane 47 daga cikin mamatan ka ‘iya tsira da ace an hana su bi ta inda gobarar ke ta’adi, ganin cewa mutane 30 sun kone ne kurmus cikin motarsu.

Fiye sa ma’aikatan kashe gobara dubu daya, suna cigaba da kokarin kashe gobarar har yanzu, wadda ke babbake yankin Pedroao Grande tun karshen makon daya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.